Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya sanar da korar kwamandan sojojin sama na kasar, kwana guda bayan da aka bayar da sanarwar faduwar wani jirgin yaki F-16 kirar Amurka da aka kai kyiv.
“Na yanke shawarar maye gurbin kwamandan Sojan Sama na sojojin sama na Ukraine,” in ji Volodymyr Zelensky a kan Telegram, bayan sanar da dokar a shafin fadar shugaban kasar.
Kafin hakan dai rundunar sojin Ukraine ta tabbatar da faduwar jirgin yakinta na F16 yayin wani aiki a cikin kasar.
Wata sanarwa da rundunar ta wallafa a shafin Telegram ta bayyana cewa, yayin da suke aiki, jiragen yaki na F16 sun lalata makamai masu linzami 4, kuma daya daga cikinsu ya bace lokacin da ya nufi aiki na gaba da zai gudanar.
Sanarwar ta kara da cewa, daga baya jirgin ya fadi kuma matukinsa ya mutu. Sai dai ba ta sanar da ainihin ranar da lamarin ya auku ba.
A farkon watan Augusta ne shugaban kasar Volodymyr Zelensky ya sanar da cewa, kashin farko na jiragen yaki na F16, kirar Amurka sun isa kasar ta Ukraine.