Zanga-zangar goyon bayan Falasdinu ta barke a Rio gabanin taron G20

Daruruwan masu zanga-zangar ne suka yi maci a bakin tekun Copacabana na Rio de Janeiro a ranar jiya Asabar, inda suka gudanar da zanga-zangar nuna

Daruruwan masu zanga-zangar ne suka yi maci a bakin tekun Copacabana na Rio de Janeiro a ranar jiya Asabar, inda suka gudanar da zanga-zangar nuna goyon baya ga Falasdinawa tare da neman a magance matsalolin duniya ta hanyoyi na lumana da zaman lafiya, wanda hakan na zuwa a daidai lokacin da ake shirin fara taron shugabannin kungiyar G20 a birnin.

Zanga-zangar ta lumana an  gudanar da ita a karkashin ruwan sama da kuma rakiyar  jami’an tsaro masu sa ido a kai, da nufin aikewa da sako ga shuwagabannin gwamnatocin da za su gudanar da babban taron koli na G20 a birnin a ranakun Litinin da Talata.

Masu zanga-zangar dai na dauke da tutocin Falasdinu da alluna masu dauke rubutu na neman kawo karshen dangantakar Brazil da “Isra’ila” da kuma dakatar da tallafin soji ga “Isra’ila” saboda kisan kare dangi da take yi a Gaza da Lebanon.

Wasu mahalarta taron, sanye da kayan na gargajiya na Larabawa  sun bi sahun kungiyoyin masu gudanar da zanga-zangar.

Tania Arantes, mamba ce daga daya daga cikin kungiyoyin da suka shirya zanga-zangar, ta shaida wa AFP cewa, “Mun zo nan ne domin nuna damuwarmu ga taron koli na G20  akan abubuwan da suke ci mana tuwo a kwarya.”

Ta yi nuni da cewa, shugabannin G20 na da karfin tattalin arziki a kan kasashen da suke ganin suna karkashinsu, ta kuma yi kira da a gaggauta yin garambawul don magance rashin daidaito a duniya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments