Zanga-Zanga Ta hana Wakilin Amurka Ziyara A Kudancin Lebanon

Masu zanga zanga za wasu yankunan kudancin kasar Lebanon sun tilastawa jakada na musamman na gwamnatin Amurka a kasar Siriya da Lebanon Tom Barrack ya

Masu zanga zanga za wasu yankunan kudancin kasar Lebanon sun tilastawa jakada na musamman na gwamnatin Amurka a kasar Siriya da Lebanon Tom Barrack ya fasa ziyarar da yake son kaiwa wasu yankuna a kudancin kasar Lebanon.

Shafin yanar gizo na labarai Arab News ya bayyana cewa mutane a garin Sur sun yi gangami a kan babban titin da ke shiga garin tare da rike hotunan shahidan Hizbullah, da kuma wasu hotuna wadanda suke kiran jakadan da suna “Dabba” ya sa Barrack ya fasa ziyarar.

Tom Barrack yana daga cikin jami’an gwamnatin Amurka suke son tilastawa shuwagabannin gwamnatin kasar Lebanon, sun kwance damar kungiyar Hizbullah na kasar da karfi. Hizbullah wacce ta dauki shekaru tana hana HKI shiga kasar kasar.

Wannan shirin nasu kamar yadda kowa ya sani budewa HKI hanya ce nan ta sake mamayar kasar ta Lebanon.  Kafin haka dao Barrack ya kwatanta yan jaridun kasar Lebanon da dabbobi. 

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments