Za’a Gurfanar Da Mutane 40  A Gaban Kotu Kan Zargin Yin Barazana Ga Tsaron Kasa A Tunisiya.

A yau ne za a gurfanar da yan adawar siyasa guda 40 da ake tuhumarsu  da aikata laifukan dake barazana ga tsaron kasa, a shari’ar

A yau ne za a gurfanar da yan adawar siyasa guda 40 da ake tuhumarsu  da aikata laifukan dake barazana ga tsaron kasa, a shari’ar da ƙungiyoyin kare hakkin bil adama suke daukarta a matsayin bi ta da kullin siyasa.

Wadanda ake tuhumar sun hada da jami’an diflomasiyya da yan siyasa da lauyoyi da kuma yan jarida dake sukar salon mulkin shugaban kasar Kais Saied.

Zargin yi wa tsaron ƙasa zagon kasa da kuma shiga kungiyar yan ta’adda zai fuskanci hukunci mai tsananin, ciki har da hukuncin kisa.

Tun a shekara ta 2023 ne ake tsare da wasu , yayin da da dama kuma suka tsere zuwa kasashen ketare.

Masu fafutukar kare hakkin bil adama sun yi kira da a gudanar da zanga-zanga a birnin Tunis don nuna adawa da shari’ar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments