Kasar Yemen ta ce ta saki ma’aikatan jirgin ruwan dakon kaya mallakin Birtaniya mai suna Galaxy Leader, wanda aka don nuna goyan baya ga Falasdinawa jim kadan bayan da Isra’ila ta kaddamar da yakinta na kisan kiyashi a zirin Gaza a watan Oktoban shekarar 2023.
Majalisar Koli ta Siyasa ta Yemen “ta ba da sanarwar sakin ma’aikatan jirgin, wadanda aka kama a ranar 19 ga Nuwamba, 2023.”
Ta ce matakin ya zo ne “domin goyon bayan tsagaita bude wuta” da aka yi a Gaza ranar Lahadi.
Wata tawagar masarautar Oman ce ta isa Sanaa babban birnin kasar Yemen domin tattaunawa da kungiyar Ansarullah don sakin ma’aikatan jirgin da kungiyar ke rike da su sama da shekara guda.
Ma’aikatan jirgin su 25 sun hada da ‘yan kasashen Bulgaria, Ukraine, Philippines, Mexico da Romania.
Kungiyar gwagwarmaya ta Ansarullah ta kaddamar da hare-hare sama da 100 kan jiragen ruwa na kasuwanci da na soji masu alaka da Isra’ila a tekun Bahar Rum.
A ranar Litinin Shugaban kungiyar Ansarullah Abdul Malik al-Houthi ya bayyana cewa a shirye suke su ci gaba da yaki da Isra’ila idan Tel Aviv ta karya yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza.