Yemen Ta Nutsarda Wani Jirgin Ruwana HKI Saboda Sabawa Haramcin Wucewa Ta Red Sea

Labaran da suke fitowa daga kasar Yemen sunn bayyana cewa sojojin ruwan kasar sun nutsar da wani karin tankar dakon mai mallakin HKI a cikin

Labaran da suke fitowa daga kasar Yemen sunn bayyana cewa sojojin ruwan kasar sun nutsar da wani karin tankar dakon mai mallakin HKI a cikin tekun Red sea. Sojojin kasar sun bayyana cewa jigin ya sabawa Haramcin don haka sun tsutsar da ita. Sun yi haka ne don nuna goyon bayansu ga al-ummar Falasdinu wadanda ake zalinta a Gaza.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa jirgin yana nufin zuwa ummu Rash Rash ko Ilat kamar yadda yahudawan suke kiransa.

Sojojin kasar Yemen sun kara da cewa sun dauki wannan matakin kan jirgin ne bayan an gargade shi da ya koma amma yaki sauraro. Da wannan talilin sojojin ruwa na kasar yemen suka yi amfani da jiragen da ake sarrafasu daga nesa suka kaiwa jirgin mai suna ;ETERNITY C hare-hare sun tare da amfani da makamai masu linzami  samfurin har  ya nutse a cikin ruwa.

Labarin ya kara da cewa basu kashe wani ba, sai dai sun kama masu aiki a jirgin zu raka su zuwam kan tudu.

Labarin ya kammala da cewa wannan halin zai ci gaba har zuwa lokacin da HKI zata daina kissan Falasdinawa a Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted