Yemen Ta Kai Wa Tel Aviv Hari Da Makami Mai Linzami Da Safiyar Yau Jumaa

Harin da sojojin Yemen su ka kai wa birnin Tel Aviv ya yi sanadiyyar jikkatar ‘yan share wuri zauna su 17 kamar yadda kafafen watsa

Harin da sojojin Yemen su ka kai wa birnin Tel Aviv ya yi sanadiyyar jikkatar ‘yan share wuri zauna su 17 kamar yadda kafafen watsa HKI su ka ambata.

Mazauna wannan birni sun firgita yayin da jiniyar gargadi ta kada a cikinsa.

Kafafen watsa labarun HKI sun ce, adadin makamai masu linzamin da aka harba daga Yemen sun kai 3, kuma sojoji sun kakkabo su, amma kuma sun ce mutane 17 sun jikkata.

Yankunan da makamai masu linzamin na Yemen su ka fada sun hada matsugunan ‘yan share wuri zauna na “Sharun’ da kuma  “Gush Dan”.

Filin jiragen sama na “Ben Gorion” ya dakatar da ayyukansa a lokacin faduwar makamai masu linzamin, inda jirage su ka daina sauka ko tashi.

Wannan dai ba shi ne karon farko da sojojin Yemen su ka kai wa Tel Aviv hari ba,inda a watannin baya su ka harba jirgi maras matuki.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments