Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ya Jaddada Cewa Falasdinawa Suna Jihadi Don Allah Ne

Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya jaddada cewa: Al’ummar Falastinu da Gaza suna gwagwarmaya ne saboda Allah Madaukaki Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewa; Mujahidan Falastinu da Gaza suna gwagwarmaya ne saboda Allah Madaukaki. Jagoran yana mai jaddada cewa: Wajibi ne dukkanin musulmi su taimaka […]

Babban Sakataren MDD Ya Ce Falasdinawa Suna Rayuwa Cikin Jahannama A Zirin Gaza

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya jaddada cewa:                 Falasdinawa suna rayuwa cikin jahannama don haka kada duniya ta wofantar da lamarinsu Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya António Guterres ya kwatanta yanayin da Falasdinawa suke ciki tare da masifar da suke fuskanta tun daga ranar 7 ga watan Oktoban shekara ta 2023, da “Jahannama da azabarta […]

Kwamnadan Dakarun Kare Juyin Juya Halin Musulunci Ya Ce Hizbullah Ce Za Ta Yi Nasara

Kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran ta bayyana cewa: Kungiyar Hizbullah ce za ta yi nasara tare da dakile shirin makiya yahudawan sahayoniyya Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na kasar Manjo Janar Hossein Salami ya jaddada cewa: Da a ce kasashen Amurka da Birtaniya da Faransa da kuma dukkan […]

Wakilan Kasashen Duniya Sun Fice Daga Zauren Majalisar Dinkin Duniya Ya Yi Jawabin Netenyahu

Wakilan kasashe da dama na duniya ciki har da Iran, sun fice               daga cikin babban zauren Majalisar Dinkin Duniya yayin jawabin fira ministan haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu Tawagogin kasashen Larabawa da na kasa da kasa da suka hada da tawagar Iran, sun fice daga cikin babban zauren Majalisar Dinkin Duniya, bayan da fira ministan […]

Sojojin Yemen Sun Kai Hare-Hare Kan Jiragen Ruwan Amurka A Tekun Bahar Maliya

Sojojin Yemen sun sanar da kai hare-hare kan jiragen ruwan Amurka guda uku a cikin tekun Bahar Maliya Kakakin Rundunar Sojin Yemen Birgediya Janar Yahya Sari’e ya sanar a yau Juma’a cewa: Dakarun kasar Yemen sun kai jerin hare-hare kan wasu jiragen yakin Amurka guda uku a tekun Bahar Maliya tare da nuna faifyai bindiyon. […]

Iran Zata Karfata Dangantakarta Da Sojojin Ruwa na Kasar Chaina

Babban kwamandan sojojin ruwa na JMI Shahram Irani wanda yake ziyarar aiki a birnin Beijing na kasar Chaina tare da tawagarsa, ya bayyana cewa gwamnatin JMI zata kara karfafa dangantaka da sojojin ruwa na kasar Chaina, saboda kara karfin sojojin ruwan kasar da kuma musayar fasaha a tsakaninsu. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran […]

Qalibof: Babban Matsalar Kasashen Yakin Asiya Ta Kudu Itace HKI

Kakakin majalisar dokoki ko majalisar shoora Islami na JMI Mohammad Bakir Qalibof ya bayyana cewa babban matsalar kasashen yankin Asiya ta kudu ita ce samuwar HKI  a yankin. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Qolibof yana fadar haka a taron kwamandojojin sojojin JMI karo na 36TH kuma a cikin ranakun makon yaki […]

Hizbullah Tana Cigaba Da Kai Wa HKI Hare-Haren Mayar Na Martani

A jiya Alhamis mayakan kungiyar ta Hizbullah sun sanar da harba makamai masu linzami a sassa daban-daban na HKI da su ka hada da kamfanin kera makamai na “Rufael a arewacin Haida. Har ila yau dakarun na Hizbullah sun kai wani harin da makamai masu linzami akan sansanin soja na “Daud” da can ne cibiyar […]

 Mahmud Abbas:  Isra’ila Ba Ta Cancanci Zama Memba A MDD Ba

Shugaban gwamnatin kwarya-kwarya ta Falasdinu Mahmud Abbas ya bayyana cewa: Ko kadan bai kamata ace an bai wa Isra’ila kujera a MDD ba, domin abinda take yi a Gaza kisan kiyashi ne. Mahmud Abbas wanda ya gabatar da jawabi a taron MDD karo na 79 ya ce; Gwamnatin Falasdinu za ta gabatar da bukata a […]

 Yemen Ta Kai Wa Tel Aviv Hari Da Makami Mai Linzami Da Safiyar Yau Jumaa

Harin da sojojin Yemen su ka kai wa birnin Tel Aviv ya yi sanadiyyar jikkatar ‘yan share wuri zauna su 17 kamar yadda kafafen watsa HKI su ka ambata. Mazauna wannan birni sun firgita yayin da jiniyar gargadi ta kada a cikinsa. Kafafen watsa labarun HKI sun ce, adadin makamai masu linzamin da aka harba […]

 Sayyid Husi: Hizbullah Tana Da Karfi Fiye Da Baya

Shugaban kungiyar Ansarullah,sayyid Abdulmalik al-Husi ya bayyana cewa; Kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon tana da karfi a wannan lokacin fiye da zamanin baya. Sayyid Abdulmalik al-Husi ya bayyana cewa; Da Lebanon da Falasdinu suna fuskantar abokin gaba ne guda daya, tare da yin ishara da laifukan yaki da HKI take tafkawa a Gaza wand aba […]