Search
Close this search box.

Yemen Ta Gargadi Saudiya Kan Barin Amurka Ta Yi Amfani Da Sararin Samaniyarta Don Kai Mata Hare Hare

Gwamnatin kasar Yemen ta bada sanarwan cewa ta aikewa gwamnatin kasar Saudiya sako na gargadi kan kada ta amincewa Amurka ta yi amfani da sararen

Gwamnatin kasar Yemen ta bada sanarwan cewa ta aikewa gwamnatin kasar Saudiya sako na gargadi kan kada ta amincewa Amurka ta yi amfani da sararen samaniyarta wajen hare haren da take kaiwa kasar.

Tashar talabijin ta Al-Masirah ta kasar Yemen ta nakalto mamba a majalisar koli ta tsaron kasar Yemen Muhammad Ali Al-Huthi yana fadar haka a jiya Lahadi.

Sojojin kasashen Amurka ta Burtania suna yakar kasar Yemen ne don tilasta mata barin jiragen ruwan HKI na kasuwanci wucewa ta babul mandab. Amma gwamnatin yaemen ta ce ba zata daina goyon bayan Falasdinawa ba sai an dakatar da bude wuta a gaza.

Muhammad Ali Huthi ya bayyana cewa sojojin kasar Yemen suna da makamin da zasu kai har kasar Amurka idan sun ga damar amfani da shi.

Daga karshen yace har yanzun yaki da saudiya bai kare na don ba’a shelanta tsagaita budewa juna wuta ba don haka idan ta kuskura ta taimakawa makiya a kanta zata sha mamaki.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments