Search
Close this search box.

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji’un: Rasuwar Shugaban Kasar Iran Da Mukarrabansa A Hatsarin Jirgin Sama  

Shugaban kasar Iran da abokansa sun yi shahada a lokacin da jirginsu mai saukar ungulu ya fado a yankin gabashin kasar Azarbaijan Labarai da dumi-duminsu

Shugaban kasar Iran da abokansa sun yi shahada a lokacin da jirginsu mai saukar ungulu ya fado a yankin gabashin kasar Azarbaijan

Labarai da dumi-duminsu suna bayyana cewa: Shugaban kasar Iran Sayyid Ibrahim Ra’isi da abokansa sun yi shahada a lokacin da jirginsu mai saukar ungulu ya yi hadari a tsaunukan gabashin Azarbaijan.

Jirgin sama mai saukar ungulu na shugaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran Sayyid Ibrahim Ra’isi ya yi hatsari, wanda ya yi sanadin hatsarin jirgin ya janyo rasuwarsa tare da abokan tafiyarsa, bayan halartar bikin bude madatsar ruwa ta Qiz Qalasi a kan hanyarsu ta komawa birnin Tabriz na Iran.

Baya ga shugaba Ra’isi, jirgin mai saukar ungulu na dauke da ministan harkokin wajen kasar Amir Hossein Abdullahian da wakilin ma’aikatar shari’a a lardin gabashin Azarbaijan da Limamin Juma’a na Tabriz, Muhammad Ali Al Hashem, da gwamnan lardin Malek Rahmati da ma’aikatan jirgin helikwaftar, da kuma daya daga cikin jami’an tsaro.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
2 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments
Hassan Adamu Rimingado
1 month ago

Allah Ya karɓi shahadar su