Yemen: Sojojin Hayar Saudia Kimani 50 Ne Suka Halaka A Shabwa

Sojojin Yemen sun aiwatar da wasu hare hare kan sansanonin sojojin hayar saudia a gabacin lardin Shabwa, inda suka halaka sojoji akalla 53 sannan wasu

Sojojin Yemen sun aiwatar da wasu hare hare kan sansanonin sojojin hayar saudia a gabacin lardin Shabwa, inda suka halaka sojoji akalla 53 sannan wasu kimani 200 kuma suka ji rauni.

Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kakakin sojojin kasar Yemen Burgedia Janar Yahyah Saree yana fadar haka, ya kuma kara da cewa sojojin na Yemen sun yi amfani da makamai masu linzami samfurin bilistic a hare haren da suka kaiwa sansanin sojojin haya na kasar ta saudia a lardin Shabwa.

Majiyar gwamnatin lardin shabwa mai bin gwamnatin tsakiya ta Aden ta bayyana cewa, makaman sojojin Yemen sun fada kan sansanin sojojin nasu ne a dai dai lokacinda suke horasda sabbin sojojin da suka dauka don yake da halattacciyar gwamnatin san’aa.

Janar Saree ya kara da cewa a Al-Suqya da Ras Al-Ara da suke Lardin Lahij sun kai hare hare har sau 6 da makamai masu linzami. Kuma sun kashe sojoji da dama wasu kuma sun ji raunuka.

A wani labarin kuma an ji karar tashin jinia a wurare da dama a kasar ta Saudia a jiya litinin saboda faduwar makaman Yemen a kansu. .

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted