Yemen Ta Zargi MDD Da Nuna Rashin Adalci A Rikicinta Da Saudiyya

Kungiyar Ansarullah wacce take iko da mafi yawan kasar Yemen, ta zargi kwamitin tsaro na MDD kan yanda yake nuna fuska biyu, a yakin da

MDD

Kungiyar Ansarullah wacce take iko da mafi yawan kasar Yemen, ta zargi kwamitin tsaro na MDD kan yanda yake nuna fuska biyu, a yakin da ke faruwa a kasar Yemen.

Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Mohammad Al-Farah wani jigo a cikin kungiyar yana fadar haka, ya kuma kara da cewa, jiragen yakin saudia suna ci gaba ta kashe fararen hula da kuma rurrusa gine gine, amma a bange guda kuma tana yin allawadai da kasar Yemen idan sun kai hare kan kasar saudia. Wadanda na maida martani ne.

Al-Farah ya bayyana cewa wannan shi ne fuska biyun da saudia take nuna a tsakanin kasashen duniya maimakon ta yi adalci.

Kafin haka dai ma’aikatar Lafiya ta kasar Yemen ta bada sanarwan cewa, tun fara wannan yakin a ranar 20 ga  watan Yulin da ya gabata, jiragen yakin Saudia sun yi sanadiyyar mutuwar mutane 124 sannan wasu 327 suka jikata a duk fadin kasar. Mafi yawansu mata da yara.

Kasashen biyu sun fara yaki ne tun watan Maris na shekara ta 2015 a lokacin kasar saudia ta farwa kasar ta Yemen da yaki don maida tsohon shugaban kasar Abdu rabu Mansur Hadi kan kujerar shugabancin kasar. Inda suka fafata na tsawon shekaru 8 ba tare da sun sami nasara ba. Sannan bayan tsagaita wuta na shekaru 4, yakin ya sake barkewa saboda yemen ta bukaci saudia ta kawo karshen takunkuman tattalin arzikin da ta dorawa kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted