Tsohon kwamandan rundunar sojin yahudawan sahayoniyya a Gaza ya ce: Sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila suna yawo a Gaza, amma a fili yake cewa Isra’ila ba za ta cimma burin da ta ayyana ba
Jaridar Ma’ariv ta haramtacciyar kasar Isra’ila ta nakalto Gadi Shamani yana cewa: Yana da wuya a cimma nasarar dawo da dukkan fursunonin yahudawan sahayoniyya daga Zirin Gaza ta hanyar nuna karfi, yana ganin cewa: Tabbas kungiyar Hamas za ta fuskanci hasara a yakin da aka kaddamar kanta, amma ba za a iya kawo karshenta ta hanyar karfin soji ba.
A cewar Shamani, gwamnatin Benjamin Netanyahu ta wurga haramtacciyar kasar Isra’ila cikin rudani da zai shafe tsawon shekaru da yawa, da zama saniyar ware a idon duniya da kuma karin fuskantar tabarbarewar harkar tattalin arziki.