Search
Close this search box.

Yemen Da Kuma Masu Gwagwarmaya A Iraki Sun Kai Hare Haren Hadin Guiwa Kan Birnin Haifa Na HKI

Sojojin Kasar Yemen tare da hadin kai da masu gwagwarmaya a kasar Iraki sun cilla makamai masu linzami kan birnin Haifa cibiyar tattalin arziki na

Sojojin Kasar Yemen tare da hadin kai da masu gwagwarmaya a kasar Iraki sun cilla makamai masu linzami kan birnin Haifa cibiyar tattalin arziki na HKI tare da amfani da makamai masu linzami samfurin cruise.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto kakakin sojojin kasar Yemen Yahyah Saree yana fadar haka a safiyar yau Laraba, ya kuma kara da cewa bararsu a hare haren hadin giwar dai shi ne jirgin Ruwan da yake sauke makamai a tashar jiragen ruwa na Haifa, ya kuma kara da cewa, sun cilla makaman linzami da dama kan jirgin kuma sun sameshi kamar yadda suka tsara.

Sojojin kasar Yemen da kuma kungiyoyi masu yaki da yan ta’adda a kasar Iraki dai suna daga cikin kawancen masu gwagwarmaya a yankin, don haka sun shiga yaki da HKI ne don tallafawa falasdinawa a Gaza, wadanda sojojin HKI suke maku kiyan kare dangi a zirin Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments