Yedioth Ahronoth: Jiragen sama marasa matuka na Hezbollah sun yi illa ga tsaron Isra’ila

Jaridar Yedioth Ahronoth ta Isra’ila ta ce sojojin Isra’ila a yanzu sun kara fahimtar kudurin da kungiyar Hizbullah ta dauka a fannin zafafa ayyukan soji

Jaridar Yedioth Ahronoth ta Isra’ila ta ce sojojin Isra’ila a yanzu sun kara fahimtar kudurin da kungiyar Hizbullah ta dauka a fannin zafafa ayyukan soji kan Isra’ila.

A cewar jaridar, hatta gungun kananan sojoji da suke aiki a cikin  mayakan kungiyar Hizbullah daga mutum uku zuwa shida suna gudanar da aiki bisa tsarin shugabanci a kan iyaka.

Ta kara da cewa, kungiyar Hizbullah ta jibge daruruwan mayaka ne kawai a fagen daga, sannan ta ajiye manya-manyan dakaru a layin bayan fage na tsawon lokaci.

A daya bangaren kuma jaridar Isra’il Hayom, ta ce jiragen da Hezbollah suka harba suna sa jami’an tsaron saman Isra’ila da sojoji kwana a farke.

Hakan na zuwa ne bayan wani jirgin mara matuki daga kasar Lebanon ya iya kutsawa cikin sararin samaniyar yankunan Falastinu da yahudawa suka mamaye ba tare da an gano shi ba, , ko kuma harbo shi.

Jirgin mara matuki ya yi nasarar yin tasiri dab a a taba ganin irinsa ba, inda ya kai hari kan gidan Firayim Ministan Haramtacciyar Kasar Isra’ila mai ci Benjamin Netanyahu a Kaisariya.

Kafofin yada labaran Isra’ila sun bayyana damuwa da fargaba game da kalubalen da jiragen yakin Hizbullah ke yi, musamman a kan sojojin tsaron saman Isra’ila.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments