Ranar 21 ga watan Augusta na ko wace shekara itace ranar masallaci ta duniya, saboda tunawa da ranar da wani bayahude ya kona masallacin Al-Aksa wanda ke birnin Kudus na kasar Falasdinu da aka mamaye.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa JMI ceta bukaci kungiyar kasashen Musulmi ta OIC ta amince da ranar 21 ga watan Augusta na ko wace shekara ta zama ranar masallaci ta duniya, saboda tunawa da ranar da Denis Michael Rohan wani Kirista kuma bayuhuden Sahyoniyya ya kona masallacin Kudus, kusa da masallacin Alkasa, wanda ya kasance wuri mai tsarki ga musulmi.
Masallacin Al-aska dai shi ne masallaci na uku a daraja a wajen musulmi, bayan masallacin Haramin Kaaba, da masallacin manzon All..(s) dake Madina.
Banda haka shi ne alkiblar musulmi ta farko kafin All..T ya sauya shi zuwa dakin ka’aba. Wannan masallacin yana da muhimmaci a wajen musulmi, kuma don muhimmancinsa ne ya sa ake samun tashe tashen hankula tsakanin musulmi da yahudawan sahyoniyya wadanda suke son rusa shi don gina Haikal na annabi sulaimanu a inda masallacin yake.