“Yar Wasan ” Taekwondo” Ta Iran Ta Sami Lambar Yabo Ta Tagulla A Wasannin Asiya Na Kasar Japan

Haka nan kuma 'yar wasan ta Iran ta buga da Dayin Sang daga kasar Korea Ta Kudu, a wasan kusa da na karshe, said ai
wasannin Asiya

Kamfanin dillancin Labarun “Irna” Ya bayar da labarin cewa; ‘yar wasan Motsa Jiki na “Taekwondo” ta kasar Iran Fatima Ahmadi ta sami lambar yabo ta tagulla a wasannin da ake yin a nahiyar Asiya a cikin kasar Japan

  Fatima Ahmadi wacce take wasa a ajin nauyi na kilo 67 na mata ta yi nasarar kai wa matakin kusa da na karshe bayan da ta sami nasarar akan ‘yan wasan kasashen  yankin Tipe na China da kuma Saudiyya.

Haka nan kuma ‘yar wasan ta Iran ta buga da Dayin Sang daga kasar Korea Ta Kudu, a wasan kusa da na karshe, said ai ba ta yi nasara ba, da hakan ta sa ta sami lambar yabo ta tagulla.

 Mata  hudu ne daga Iran da suka shiga cikin wasannin Asiya na Garin Nagoya a kasar Japan, daya ta sami zinariya, sai kuma wata da ta sami tagulla, yayinda da biyu aka fitar da su.

 Shugaban Kasar Iran Ya Yaba Wa ‘Yan Wasan Kasar Saboda Nasarorin Da Suke Samu A Wasannin Asiya A Kasar Japan

Shugaba Mas’ud Pezeshkiyan ya wallafa sako a shafinsa na Sada zumunta da a ciki ya yi yabo da jinjina ga ‘yan wasan da suke wakiltar kasar a wasannin Asiya a kasar Japan.

Ya zuwa yanzu dai ‘yan wasan na kasar Iran sun sami lambobin yabo 45 da su ka kunshi zinariya, azurfa da tagulla.

Kasashen da suke gaban Iran guda hudu su ne China, Japan, Korea Ta Kudu da Kuma Uzbekistan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted