Bangarori mabanbanta na kasar Lebanon suna mayarwa da ‘yar sakon Amurka martani saboda tsoma baki da ta yi a kan yadda za a kafa gwamnati a kasar.
Morgan Ortagus wacce ta gana da jami’an kasar Lebanon ta bayyana cewa, bai kamata a kafa gwamnati a kasar ta wakilan kungiyar Hizbullah a ciki ba.
Kungiyar malaman addinin musulunci ta fitar da bayani da a ciki ta ce; “Furucin mataimakin manzon Amurka a gabas ta tsakiya, Morgan Ortagus wacce ‘yar sahayoniya ce,tsoma baki ne a harkokin cikin gidan Lebanon wanda ya tsallake ka’idojin aikin diplomasiyya.”
Ita ma gwamnatin kasar ta Lebanon ta fitar da bayani tana mai cewa abinda Ortugas din ta furta, ra’ayinta ne, bai shafi gwamnatin Lebanon ba.
Shi kuwa shugaban kungiyar ‘yan majalisar dokokin Lebanon masu wakiltar Hizbullah, Muhammad Ra’ad ya bayyana furucin na ‘yar sakon Amurkan da cewa; Hikidi ne da kuma tsoma baki a harkokin cikin gidan Lebanon.