Yansanda a birnin Lagos na kudancin kasar sun kama wasu yan kasar Pakistan biyu wadanda suke da hannu dumu-dumi a cikin aikin kamawa don neman kudaden fansa daga hannun wani dan kasar ta Pakistan dan shekara 48 a duniya.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran sun nakalto daga kafafen yada labaran kasar wadanda suka ji kakakin yansan na jihar Lagos Chief Superintendent Benjamin Hundeyin yana cewa, yan kasar Pakisatn da suka kama a wani dauki da suka wanda aka sace don neman kudaden fansa sun kama a ranar 5 ga watan maris akwia Roman Gull dan shekara 19 da kuma Aftab Ahmed dan shekarera 28 a duniya kuma yan asalin kasar Pakistan ne, wadanda suka hada kansu da wasu gungun barayi don yin haka.
Ya ce barayin sun nemi dalar Amurka $34,000 ko naira miliyon 50 daga wajensa a matsayin kudaden fansa. Amma kamfanin da yake yiwa aiki sun bada naira miliyon guda kacal a cikin kwanaki uku, inda yan sanda suka shiga suka kuma kubutar da shi. Kuma yansanda suna kokarin gano sauran mutane 5 da suke rage cikin gungun yan fashin.