Rahotannin kafar watsa labaru ta “Parstoday’ ta bayyana cewa, Iran ta aike da tawaga ta ‘yan wasan “Taekwondo” idan ake fafatawa da su a wasannin da ake yi a birin Paris na kasar Faransa.
‘Yan wasan matan su biyu su ne; Nahida Kiyani ‘yar shekaru 25 da Mubinah Ni’imat Zadeh ‘yar shekaru 18.
A wasannin nahiyar Asiya, wadannan ‘yan wasan biyu sun samowa Iran lambobin zinariya a baya.
A shekarar ta da ta gabata 2023 Nahida ta sami nasarar samun lambar yabo ta zinariya a ajin nauyin kilogram 53.
Ita kuwa Mubinah Ni’imat Zadeh, ta taba samun lambar yabo ta zinariya ne a wasannin da aka yi a 2022.