‘Yan Tawayen Sudan Sun Kashe ‘Yan Gudun Hijira Da Suke Shirin Komawa Muhallinsu

Dakarun Kai Daukin Gaggawa ta Rapid Support Forces a Sudan sun kashe rayukan mutanen da suke kan hanyar komawa gidajensu a yankin Darfur Rahotonni sun

Dakarun Kai Daukin Gaggawa ta Rapid Support Forces a Sudan sun kashe rayukan mutanen da suke kan hanyar komawa gidajensu a yankin Darfur

Rahotonni sun tabbatar da cewa: An kashe kimanin ‘yan Sudan 20 da suka rasa matsugunansu a ranar Alhamis, 4 ga Yuli, a kan hanyar hamada da ta haɗa yankin Al-Tina da ke yammacin Sudan da birnin Ad-Dabba a arewa, a cikin mummunan bala’in da ya afka wa waɗanda suka tsere daga mummunan yaƙin yankin Darfur.

A cewar rahotannin da aka samu, sun bayyana cewa lamarin ya faru ne lokacin da wasu matasa ke tafiya daga Al-Tina zuwa Ad-Dabba. Wasu mutane dauke da makamai da ke da alaƙa da Rundunar Rapid Support Forces ta Dakarun Kai Daukin Gaggawa (RSF) suka tare su, waɗanda suka buɗe musu wuta ba tare da wani laifi ba. Har yanzu ba a san makomar wasu daga cikin wadanda suka tsere ba.

Wannan lamarin ya faru ne makonni biyu bayan kisan mutane takwas da suka rasa matsugunansu a kan hanya ɗaya, a daidai lokacin da Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargaɗin cewa ana ci gaba da kai hare-hare kan fararen hula a yammacin Sudan, a cewar wani rahoto da Ofishin Majalisar Dinkin Duniya kan Harkokin Jin Kai (OCHA) ya fitar a ranar 5 ga watan Yulin wannan shekara ta 2026.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted