Yan Takarar Shugaban Kasa A Iran Zasu Yi Muhawarar Farko A Tsakaninsu

Yan takarar shugaban kasa 6 a nan Iran zasu gudanar da muhawara a tsakaninsu a karon farko a yammacin yau litinin. Kamfanin dillancin labaran IP

Yan takarar shugaban kasa 6 a nan Iran zasu gudanar da muhawara a tsakaninsu a karon farko a yammacin yau litinin.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa muhawarar wanda za’a watsa ta kai tsaye shi ne na farko, sannan za’a gudanar da wasu guda 4 nan gaba.

Labarin ya kara da cewa ana bukatar ko wani dan takara ya bayyana shirinsa na warware matsalolin da kasar ta ke fama da su. Da kuma mahangarsa a kan yadda harkokin siyasar kasar suke tafiya a halin yanzu.

Yan yakaran dai sun hada da shugaban majalisar dokokin kasar mai ci Muhammad Bakir Kolibof, Sa’eed Jalili, Masud Pezeshkian, Mostafa Purmohammadi, Amir-Hossein Kazizaadeh Hashemi, da  kuma Alireza Zakani.

Hukumar radiyo da talabijin na kasar Iran ta shirya irin wannan muhawarar har guda 5 ga yan takarar shugaban kasa guda 6, kuma sun hada da nay au 17, ga watan yuli, 20,21,24 da kuma 25 ga watan. Za’a gudanar da zaben shugaban kasa karo na 14 a nan kasar Iran ne a ranar 28 ga watan yunin da muke ciki.

Za’a gudanar da zaben shugaba a kasar Iran a wannan karonn ne, saboda rasuwar marigiyi shugaba Ibrahim Ra’isi a wani hatsarin jirgin sama a ranar 19 ga watan Mayun day a gabata.

Kundin tsarin mulkin kasar ya bukaci a gudanar da zaben shugaban kasa cikin kwanaki 50 kacal bayan rasuwa ko saukar shugaban kasa daga mukaminsa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments