‘Yan Share Wuri Zauna 1000 Ne Su Ka Kutsa Masallacin Kudus

Kwanaki uku a jere kenan yahudawa ‘yan share wuri zauna suna kutsawa cikin farfajiyar masallacin kudus adaidai lokacin da suke bikin idul-Arsh” da suke daukar

Kwanaki uku a jere kenan yahudawa ‘yan share wuri zauna suna kutsawa cikin farfajiyar masallacin kudus adaidai lokacin da suke bikin idul-Arsh” da suke daukar mako daya suna yi.

Hkumar da take kula da cibiyoyin musulunci da suka hada da masallacin Kudus, ta bayyana cewa, fiye da ‘yan share wuri zauna 900 ne su ka kutsa cikin masallacin kudus,gabanin sallar Azahar a yau Laraba.

Hukumar ta kara da cewa, a cikin wannan makon kadai adadin ‘yan share wuri zauna da su ka kutsa cikin masallacin kudus da cewa sun kai 5,600.

Daga cikin wadanda suke yin kutsen da akwai ministoci da shugabannin kungiyoyin ‘yan sahayoniya mafi wuce gona da iri.

Jami’an tsaro ne suke yi wa masu kutsen cikin masallacin na Kudus rakiya saboda ba su kariya.

Tun a ranar Alhamis din da ta gabata ne dai idin na ‘yan sahayoniya ya fara, yau ne kuma yake zuwa karshe.

Shi dai idin “Arsh” yana da alaka ne da lokacin da yahudawa su ka yi zaman dirshan a cikin hemomi da karkashin inuwa a saharar Sina, saboda dimuwar da su ka yi ta tsawon shekaru arba’in, da kuma saukar musu da tsuntsun salwa da Man. Wannan lokacin ne farkon shekarar noma a wurin yahudawa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments