Jiragen saman yakin sojojin ‘yan mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila sun kaddamar da farmaki kan garuruwan Maroun al-Ras da Aitaroun, yayin da suka yi luguden bama-baman da aka kera su da sinadarin phosphorus kan garin Deir Mimas da ke kudancin kasar Lebanon.
Wannan dai na zuwa ne bayan da jami’an agaji 3 suka yi shahada, yayin da wasu 2 suka jikkata a kudancin kasar Lebanon, bayan wani farmaki da sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai kan motar kashe gobara na jami’an tsaron fararen hula a lokacin da suke kokarin kashe gobarar da sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila suka tayar a yankin. Shafin sadarwa na yanar gizo na kasar Lebanon ya ce: Sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila sun kaddamar da wani hari kan garin Faroun da ke gundumar Nabatiyah a kudancin kasar ta Lebanon, inda suka nufi wata motar kashe gobara ta fararen hula, lamarin da ya yi sanadin shahadar mutane da dama da kuma jikkata wasu na daban.