Wasu mambobi a jamaiyar Demucrat a majalisar congress din Amurka sun yi Allah wadai da duk wani yunkurin sake bude wani sabon yaki da ya sabama doka akan kasar Iran, kuma sun gargardi shugaban Amurka Donald Trump na sake kaddamar da wani yaki da ya sabama doka da jamhuriyar musulunci ta iran domin zai zamo wani babban balai ne.
Yan Demokrat din sun fito fili sun sun soki trump kuma sun zarge shi da shure dokar da ta takaita karfin shugaban kasa na fara yaki, da kuma karkatar da hankulan alumma kan daukar matakin soji kan kasar iran, kuma yana kokarin ci gaba da yaki ba tare da izinin majalais ba.
Wannan sukar ta zo ne bayan da Trump ya sanar da congress a hukumance a cikin wannnan makon cewa Amurka ta shiga wani sabon yaki da kasar iran
Ana shi bangaren shugaban yan majalisar Demukrat a congress chuck schumer yayi tir da bude sabon yakin akan iran, kuma ya rubuta a shafinsa na X cewa dole ne trump yayi aiki da kuri’ar da aka kada a majalisa na janye dukkan dakarunmu daga cutarwa kuma a kawo karshen yankin yanzu nan.