‘Yan gwagwarmayar kungiyar Hizbullahi sun kai wasu jerin hare-hare kan sassa daban-daban na haramtacciyar kasar Isra’ila
Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta kasar Lebanon ta sanar da ci gaba da kai hare-hare kan sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila da suke kokarin kutsawa cikin yankunan Falasdinawa da wuraren tarukansu a yankunan Falastinawa da suka mamaye, domin jaddada goyon baya ga al’ummar Falastinu da suke ci gaba da tsayin daka a yankin Zirin Gaza, da kuma goyon bayan ‘yan gwagwarmaya da suke ci gaba da jajircewa gami da kare kasar Lebanon daga kutsen ‘yan mamaya.
A cikin jerin bayanan kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullahi ta kasar Lebanon ta sanar da kai hare-hare kan sansanonin sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila a arewacin Falastinu da aka mamaye da wasu matsugunan yahudawan sahayoniyya ‘yan kaka gida da kuma sansanonin sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila da suke Safad da Haif da kuma Acre), baya ga kai hare-haren kwantan bauna da mayakan kungiyar suka yi wa sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila da suke kokarin sulalewa cikin Lebabon ta hanyar kudancin kasar ta Lebanon.