‘Yan Gwagwarmayar Falasdinu Sun Tarwatsa Tankokin Sojin Yahudawa Biyu A Harin Kwanton Bauna

‘Yan gwagwarmayar Falasdinawa sun tarwatsa tankokin yakin ‘yan mamaya guda biyu a wani harin kwantan bauna da suka kai musu ‘Yan gwagwarmayar Falasdinawa suna ci

‘Yan gwagwarmayar Falasdinawa sun tarwatsa tankokin yakin ‘yan mamaya guda biyu a wani harin kwantan bauna da suka kai musu

‘Yan gwagwarmayar Falasdinawa suna ci gaba da gudanar da ayyuka na musamman a fagagen yaki daban-daban a Zirin Gaza, a karkashin yakin “Ambaliyar Al- Aqsa”, a matsayin mayar da martani ga hare-haren da sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila suke ci gaba da kai wa Falasdinawa.

Dakarun Izzuddeen al-Qassam bangaren sojin kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas sun sanar da cewa: Sun kai hari kan tankokin yaki Merkava biyu na sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila da makamai masu linzami kirar “Al-Yassin 105” a kusa da Masallacin Al-Sarat da ke unguwar Al-Geneina a birnin Rafah dake kudancin Zirin Gaza.

Har ila yau, Dakarun na Al-Qassam sun wallafa wani faifan bidiyo da ke nuna yadda suka tarwatsa wani ayarin sojan kafa a wani mummunan harin kwantan bauna da suka kai a shiyar gabashin Sansanin Jabaliya da ke kudancin Zirin Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments