An kashe wani bayahuden sahayoniyya tare da raunata wani na daban a wani hari da a kai a kwarin Jordan da ke yammacin gabar kogin Jordan
Rahotonni sun bayyana cewa: Wani tsageran bayahuden sahayoniyya ya halaka, yayin da wani na daban ya samu raunuka, sakamakon harbin da aka yi kan motarsu a yankin gabar yamma da kogin Jordan, kuma maharin ya samu nasarar tserewa daga wurin.
Shafin watsa labarai na yahudawan sahayoniya “Doron Kadosh” ya bayyana cewa: Motar da take dauke da maharani da suka yi harbin ta tsere daga wurin, kuma sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila suna ci gaba da farautar su.
A gefe guda kuma, majiyar dakarun Izzuddeen Al-Qassam bangaren sojin kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta dauki alhakin kai harin.