‘Yan Gwagwarmaya Sun Halaka Sojojin Mamayar Isra’ila Uku Tare Da Jakkata Wasu Uka Na Daban

Sojojin mamayar Isra’ila uku ne aka kashe a Gaza, Netanyahu ya bayyana hakan a matsayin maraice mai wahala Rundunar sojin haramtacciyar kasar Isra’ila ta amince

Sojojin mamayar Isra’ila uku ne aka kashe a Gaza, Netanyahu ya bayyana hakan a matsayin maraice mai wahala

Rundunar sojin haramtacciyar kasar Isra’ila ta amince da cewa an kashe sojojinta uku tare da jikkatan wasu uku na daban ciki har da wani jami’in sojin a wani harin kwantan bauna da ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa suka kai kan yankin arewacin zirin Gaza.

Gidan rediyon sojojin mamayar Isra’ila ya nakalto majiyar soji na cewa; Sojojin mamayar Isra’ila uku ne suka halaka da wasu da suka jikkata cikin har da wani jami’in sojin kuma dukkansu sun fito ne daga birgediya ta 401, kuma sun halaka ne a cikin tankinsu a Jabalia da ke arewacin zirin Gaza.

Shafukan yanar gizo na labaran Isra’ila sun sanar a yau litinin cewa sojoji uku ne suka halaka sannan wasu uku suka samu munanan raunuka a hare-hare da ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa suka kai musu a zirin Gaza.

A cewar wadannan shafukan yanar gizo, gwagwarmayar Palastinawa ta afkawa sojojin mamaya a lokaci guda a Khan Yunis, Jabalia, da kuma unguwannin Al-Tuffah da Shuja’iyya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted