Tsohon babban kwamandan dakarun IRGC na kasar Iran Mohsen Rezae ya bayyana cewa yakin gaza ko na tufanul aksa ta wargaza dukkan shirin HKI da kuma tunaninta a gabas ta tsakiya.
Ya ce duk tare da amfani da karfi mafi muni kan al-ummar gaza, tare da kissan Falasdinawa fiye da 47,000 amma ta kasa samun nasara a kansu. Ya kuma zama mata dole ta sulhunta da kungiyar Hamas, wacce a farkon yakin tace sai ta ga bayanta, don dawo da yahudaw 240 da suke tsare a hannuta.
Mohsen Rezae ya bayyana haka ne a lokacinda yake hira da tashar talabijin ta Almayadeen ta kasar Lebanon.
Don haka yakin gaza ta maida HKI a matsayin kasa wacce bata da wata mahanga dangane da samuwarta nan gaba ba. Kuma bata san makomarta a yankin ba.
Yace kasa wacce ta kasa kubutar da fursinoninta a Gaza, sai tare da amincewa da sharuddan kungiyar Hamas, wannan ya tabbatar da cewa bata san makomanta a wannan yakin nan gaba ba.
Rezae dai ya na daga kwarraru masu bawa Jagoran juyin juya halin musulunci Imam Sayyid Aliyul Khaminae shara a kan al-amuran tsaro, ya na daga cikin dakarun IRGC wadanda suka shiga cikin shirin hare-haren da Iran ta kaiwa HKI a cikin watan octoban shekara ta 2023.