Wata Kotu A Amurka Ta Bukaci A Saki Wani Malami Mai Goyon Bayan Palasdinawa A Jami’ar Georgetown academic

A wata koma baya ga shirin gwamnatin Trump na dirar mikiya a kan Amurkawa magoya bayan Falasdinawa a Jami’o’iin Amurka, wata kotu ta kare hakkin

A wata koma baya ga shirin gwamnatin Trump na dirar mikiya a kan Amurkawa magoya bayan Falasdinawa a Jami’o’iin Amurka, wata kotu ta kare hakkin bil\adama ya yanke hukuncin sallamar Dr. Khan Suri malami a Jami’ar Georgetown ta Amurka wanda jami’an tsaro na shige-da fice suka kama a cikin makonnin da suka gabata saboda jawabin da yayi a taron gangami na goyon bayan Falasdinawa.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kotun ta gwamnatin tarayya ta bukaci jami’an custom da kuma shige da fice na AMurka (ICE) suka sake Dr Khan Suri daga inda suke tsare da shi makonni 8 da suka gabata, ya koma Texas inda yake zama tare da iyalansa, daga Viginia inda ake tsare da shi.

A makon da ya gabata dai alkalin kotun na gwamnatin tarayya ya ki amincewa da bukatar gwamnatin Trump na kutun ta yi watsi da sha’ar Dr Khan Suri, ko kuma ta kaurad da shari’ar zuwa Texas don shari’ar ta fice daga jihar Viginia.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments