Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Hind Rajab ta gabatar da bukatar fitar da sammacin kame ministan harkokin wajen haramtacciyar kasar Isra’ila Gideon Sa’ar da yake ziyara a Birtaniya.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa: Cibiyar Hind Rajab Foundation da ta mayar da hankali kan neman gurfanar da sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila da ake zargi da aikata laifukan yaki, ta mika bukatar kama Gideon Sa’ar a birnin Landan na Birtaniya.
Kafofin watsa labaran haramtacciyar kasar Isra’ila sun jiyo ofishin ministan harkokin wajen haramtacciyar kasar Isra’ila na cewa babu wata niyyar takaita ziyarar Sa’ar a Biritaniya ko kuma sauya jadawalinsa sakamakon wannan bukata.
A cikin wata sanarwa da cibiyar Hind Rajab ta fitar ta ce: Tana ci gaba da kokarin ganin an fitar da sammacin gaggawa kan kame Sa’ar, mamba a majalisar ministocin tsaron gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila.
Cibiyar ta yi ikirarin cewa: Gideon Sa’ar ya taimaka tare da karfafa aiwatar da laifuka da suka hada da keta dokokin jin kai na kasa da kasa a Falasdinu, ciki har da azabtarwa, kisa da gangan da kuma lalata dukiyoyi.