Kwamiti mai kula da al-amuran harkokin waje a kasar Burtaniya tana matsawa sakataren harkokin wajen kasar David Lammy kan cewa ya amince da kasar Falasdinu mai zaman Kanata.
Jaridar Telegram ta kasar Burtaniya ta nakalto wannan rahoton a yau Laraba, ta kuma kara da cewa Dan majalisa Emily Thomberrry ya kara da cewa wannan mataki na farko ne, idan Lammy ya bada wannan sanarwan a cikin wata mai zuwa a lokacin haduwarsa da Saudiya da Faransa a wani babban taro wanda zai bada damar daukar matakai nag aba.
Jaridar tace, wannan maganar tana zuwa ne bayan da sakataren ya dakatar da tattaunawa ta harkokin kasuwanci da HKI, da kuma kiran jakadan HKI a London don gabatar da korafinsa kan sake komawa yakin da gwamnatin HKI ta yi bayan an fara aiwatar da sulhun da aka amince da shi.
A babban zaben da ya gabata dai jam’iyyar Lebour ta ce zata amince da kasar Falasdinu mai cikeken yenci bisa fahintar samar da kasashe biyu. Amma benyamin natanyaho firai ministan HKI ya sha alwashin hana samuwar kasar Falasdinu kwata-kwata.
Yan majalisa ThornBerry ya fadawa Telegram kan cewa, a ra’ayinsa Burtaniya da Faransa sun amince da kafuwar kasar Falasdinu a taron Newyork wanda kasar Saudiya zata jagoranta a cikin watan Yuni mai zuwa.