Wani tsohon ma’aikacin hukumar leken asiri ta CIA ta kasar Amurka John Kiriakou ba ce a yakin kwanaki 12 tsakanin HKI da JMI, Isra’ila ta yi barazanar jefawa JMI makaman Nukliya idan har Amurka bata kai hare-hare kan cibiyoyin makamashin Nukliya na kasar Iran ba.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran, ya nakalto Mr John Kiriakou yana fadar haka a cikin makon da ya gabata. Ya kuma kara da cewa saboda wannan barazanar ce gwamnatin shugaba Trump ta kaiwa cibiyoyin makamashin Nukliya na kasar Iran wadanda suke Fordo, Natanz da kuma Esfahan. Ya ce shugaban yana ganin hare-haren da ya kaiwa cibiyoyin yafi sauki idan an kwatanta da makaman nukliya wadanda HKI ta yi barazanar zata yi amfani da su kan Iran.
Ya ce da HKI ta yi gabata ta fara amfani da makaman Nuklkiya a kan kasar Iran, da yanzu an fara yakin duniya na uku.
HKI dai ta ki ta rattabawa yarjeniyar NPT ta hana yaduwar makaman Nukliya hannu, don kada ta bawa Jami’an hukumar IAEA damar gudanar da bincike dangane da shirin nata na makaman nukliya.
Kasashen yamma musamman Amurka da Jamus sun taimaka HKI mallakan makaman Nukliya tun shekaru 1950 zuwa sama, sannan an tabbatar da cewa ta mallaki irin wadan nan makaman a cikin shekaru 1970 zuwa sama.