Wani Masanin Harkar Soji Ya Bayyana Dalilan Da Suka Wurga Sojojin Mamaya Cikin Tsaka Mai Wuya

Wani masanin harkar soji ya bayyana dalilan da suke janyo munanan hasarori da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke yi a kudancin Lebanon Masanin harkokin soji

Wani masanin harkar soji ya bayyana dalilan da suke janyo munanan hasarori da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke yi a kudancin Lebanon

Masanin harkokin soji Birgediya Janar Hassan Jouni ya bayyana cewa: Tarin hasarori da sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila suka yi a kudancin kasar Lebanon, yana shafar karfin sojojin da kwarjininsu da al’ummar Isra’ila, da kuma rusa amfanin yakin da suke yi a arewacin haramtacciyar kasar Isra’ila.

A hirarsa da tashar talabijin ta Aljazeera, Jouni ya alakanta hakan da tsayin dakan mayakan gwagwarmaya da kuma kwarewarsu wajen yakin ta kasa, baya ga masaniyarsu da yanayin yankunansu da kuma amfani da makaman da suka dace.

Jouni, wani Birgediya Janar mai ritaya ne daga sojojin kasar Lebanon, ya sanar da harin makami mai linzami na baya-bayan nan da kungiyar Hizbullah ta kai kan wani taron sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila na bataliya ta 89 da ke yankin gabas maso kudancin kasar Lebanon, yana mai bayyana abin da ya faru a wannan bataliyar a matsayin babban koma baya da ya halaka sojojin masu yawa baya ga jikkata wasu kimanin 24 na daban.

Kamar yadda rundunar sojin haramtacciyar kasar Isra’ila a yammacin jiya alhamis ta furuci da kashe hafsoshi da sojoji 57 a yankin Lebanon tun bayan barkewar arangama, ciki har da 10 da suka mutu a cikin sa’o’i 24 da suka gabata.

Sanarwar ta haramtacciyar kasar Isra’ila ta zo ne kwana guda bayan da kungiyar Hizbullah ta sanar da cewa ta yi sanadin halakar sojojin Isra’ila 70 tare da raunata wasu fiye da 600 daga cikin jami’an mamaya da sojojinsu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments