Kwamandan rundunar Gaza ta HKI Brigadier General Avi Rosenfeld ya yi murabus daga mukaminsa kwanan guda bayan da Benny Gantz daya daga cikin mambobi a kwamitin yani na gaza ya fice daga kwamitin.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ya bayyana cewa bayan ficewar Benny Gantz daga kwamitin yaki da kwana guda kwamandan rundunar gaza ya ajiye mukaminsa saboda ya gaza a yakin da kungiyar Hamas ta dorawa HKI a ranar 7 ga watan Octoban day a gabata.
General Avi Rosenfeld ya bayyana haka ne a wasikar da ya rubutawa babban hafsan hafsoshin sojojin mamayar, ya kuma kara da cewa rundunarsa ta 143 ta kasa samun nasara a kan mayakan Hamas wadanda suka kutsa cikin matsugunan yahudawa da suke gewayen gaza, suka kashe wasu daga cikin sojojinsa suka lalata makaman rundunarsa sannan suka kama wasu sojoji suka tafi da su cikin gaza.
Wannan dai shi ne murabus na biyu babba wanda aka yi daga gwamnati da kuma rundunar sojojin yahudawan Sahyoniyya yan mamaya.