Unrwa: Tun Bayan Yakin Duniya Na Biyu Ba  A Taba Kai Hare-hare Masu Tsanani Ba Kamar Na Gaza A Yanzu

Hukumar Agaji ta Unrwa; wacce take karkashin MDD ta ce, tun bayan yakin duniya da aka yi a tsakanin 1939 zuwa 1945, ba a taba

Hukumar Agaji ta Unrwa; wacce take karkashin MDD ta ce, tun bayan yakin duniya da aka yi a tsakanin 1939 zuwa 1945, ba a taba kai hare-hare masu tsanani akan wani wuri ba,kamar wanda ake yi  a wannan lokacin akan Gaza.

 A yau Juma’a ne  da take a matsayin ranar nuna goyon baya ga al’ummar Falasasdinu ta duniya,  hukumar agajin ta MDD ta fitar da wannan sanarwar tana mai jaddada cewa abinda haramtacciyar Kasar Isra’ila take yi kisan kiyashi ne.

Unrwa ta kuma ce;Har yanzu duniya ba ta iya warware wahalhalun da ‘yan hijiar Falasdinawa suke ciki ba,ga shi kuma Isra’ila tana cigaba da rusa gidajen Falasdinawa a arewacin Gaza.

A jiya Alhamis ma da hukumar ta Unrwa ta ce mutanen da adadinsu yake tsakanin 65,000 zuwa 75,000 suna fuskantar mutuwa da kaso  mai yawa a arewacin Gaza.

Wani sashe na sanarwar Unrwa da ta wallafa a shafinta na X, ta ce, sau 91 MDD ta yi kokarin kai kayan agaji cikin Gaza tun daga 7 ga watan Oktoba, sau 25 ne aka amince,amma sau 82 aka ki  amincewa.

A ranar Laraba din da ta gabata dai Unrwa ta sanar da cewa, yunwar da mutanen Gaza suke fama da ita, ta yi tsanani,kuma kullum al’amurra sake tabarbarewa suke yi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments