Search
Close this search box.

UNRWA: Isra’ila Ta Rusa Kashi Bisa Uku Na Dukkanin Ababen More Rayuwa A Gaza

Hukumar ba da agaji ta Majalisar Dinkin Duniya UNRWA ta sanar da cewa, kashi biyu bisa uku na ababen more rayuwa na Gaza sun lalace

Hukumar ba da agaji ta Majalisar Dinkin Duniya UNRWA ta sanar da cewa, kashi biyu bisa uku na ababen more rayuwa na Gaza sun lalace sakamakon hare-haren da gwamnatin sahyoniya ta kai. Kungiyar ta jaddada bukatar daukar mataki cikin gaggawa don hana afkuwar bala’o’i a yankin.

Kamfanin dillancin IRNA ya bayar da rahoton cewa, Hukumar Ba da Agaji da Ayyuka ta Majalisar Dinkin Duniya (UNRWA) ta rubuta a cikin wani sakon da ta wallafa a shafin intanet na X cewa: Tare da ci gaba da yaduwar cututtuka da karuwar  yanayin zafi, rashin tsaftar muhalli da rashin ruwa sha mai tsafa hakan na haifar da babbar barazana ga lafiyar al’ummar Gaza.

UNRWA ta kuma sanar da cewa a cikin watanni 9 da suka gabata, kusan kashi 67% na wuraren ruwa da najasa da ababen more rayuwa a zirin Gaza sun lalace sakamakon hare-haren Isra’ila.

Wannan kungiya tana taka muhimmiyar rawa wajen samar da ayyukan ceton rai ga ‘yan gudun hijirar Falasdinu.

Ta ce, lalata da muhimman ababen more rayuwa da aka yi a baya-bayan nan a Gaza na kara ta’azzara mawuyacin halin da ake ciki, kuma da yawa daga cikin mutanen Gaza ba sa samun hatta tsaftataccen abincin da zasu.

Sakamakon Yin watsi da kudurin kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da ya bukaci a tsagaita bude wuta cikin gaggawa da Isra’ila ta yi, shi ne babban dalilin hakan, maimakon yin aiwatar da kudirin ma Isra’ila na ci gaba da kai munanan hare-hare a zirin Gaza, wanda ke fuskantar tofin Allah tsine daga kasashen duniya.

A cewar jami’an kiwon lafiya na yankin, kusan Falasdinawa 37,400 ne suka yi shahada a Gaza tun daga lokacin da Isra’ila ta fara kai hare-hare, yawancinsu mata da yara, yayin da wasu fiye da 85,000 suka jikkata.

Koton hukunta manyan laifuka ta duniya na zargin Isra’ila da aikata kisan kiyashi a Gaza, sannan  kuma wannan kotun ta umarci gwamnatin yahudawan da ta gaggauta dakatar da ayyukan yaki  a Rafah, inda Falasdinawa sama da miliyan guda suka fake, amma duk da haka Isra’ila na ci gaba da yin gaban kanta wajen kashe fararen hula  ayankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments