Unifil Tana Tunanin Fara Kare Kanta Daga Hare-haren Sojojin HKI

Rundunar tabbatar da zaman lafiya ta MDD dake kasar Lebanon ( UNIFIL) ta sanar a yau Juma’a cewa; A  watannin baya ta  sami burbushin (Phosphorus

Rundunar tabbatar da zaman lafiya ta MDD dake kasar Lebanon ( UNIFIL) ta sanar a yau Juma’a cewa; A  watannin baya ta  sami burbushin (Phosphorus )  a kusa da daya daga cikin sansanoninta,wanda makami ne da aka hana amfani da shi a duniya.

Kakakin rundunar ya kuma ce, sojojin na zaman lafiya da adadinsu ya kai 10,000 za su cigaba da zama a Lebanon duk da hare-haren da sojojin Isra’ila suke kai musu, tare da kara da cewa, suna yin hakan ne cikin ganganci.

Kakakin rundunar sojan na MDD a Lebanon ya kuma ce, da akwai yiyuwar su fara aiki da dokar kare kansu daga hare-haren na sojojin HKI, amma dawo da zaman lafiya ya fi muhimmanci,sannan ya jaddada cewa suna a Lebanon babu inda za su je.

HKI ta dade tana son ganin sojojin na MDD sun fice daga kasar Lebanon, inda a kwanakin bayan nan ma ta kiraye su, da su janya daga inda suke zuwa kilo mita 5 a gaba.

 Sai dai kasashen da suka tura sojojin na MDD sun ki amincewa da bukatar ta HKI ,inda a bayan nan kasar Italiya ta sanar da cewa; kasashe 16 masu sojoji a karkashin UNIFIL, ya zama wajibi su  yi aiki da dokokin da su ka dace domin samar da hanyar da tafi dacewa na aikinsu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments