UNHR: Dole ne a gudanar da bincike kan harin Isra’ila a kusa da asibitin Beirut

Kwamishinan kare hakkin bil adama na Majalisar Dinkin Duniya, Volker Turk, ya yi kira da a gaggauta gudanar da bincike kan wani harin da Isra’ila

Kwamishinan kare hakkin bil adama na Majalisar Dinkin Duniya, Volker Turk, ya yi kira da a gaggauta gudanar da bincike kan wani harin da Isra’ila ta kai kusa da wani asibiti a kudancin Beirut fadar mulkin kasar Lebanon.

A cikin wata sanarwa a ranar Talata, Kwamishinan kare hakkin bil adama na Majalisar Dinkin Duniya ya jaddada cewa asibitoci, motocin daukar marasa lafiya, da ma’aikatan lafiya suna da kariya a karkashin dokar jin kai ta kasa da kasa, saboda muhimmiyar rawar da suke takawa wajen ceton rayuka.

Ya jaddada bukatar dukkan bangarorin su tantance tasirin ayyukan soji a kusa da asibitoci, tare da bin ka’idojin daidaito da kuma taka-tsantsan. Ya kuma bayyana cewa “dole ne a dauki dukkan matakan da suka dace don kauce wa hasarar rayukan farar hula a lokacin abin da ya kira ayyukan soji.

Yayin da yake ambato rahotannin da ke nuni da cewa yara hudu na daga cikin akalla mutane 18 da suka rasa rayukansu a harin, yayin da wasu 60 suka jikkata, jami’in ya ce “na yi matukar kaduwa,” ya kara da cewa “dole ne a mutunta muhimman ka’idoji da dokokin jin kai na kasa da kasa da suka shafi kare fararen hula.”

A jiya, kakakin sojojin Haramtacciyar Kasar Isra’ila ya yi zargin cewa Hezbollah ta ajiye miliyoyin zinariya da tsabar kudi” a karkashin asibitin al-Sahel da ke yankin kudancin Beirut.

Yawanci Isra’ila kan yi amfani da irin wadanann kalamai ba tare da wata hujja ba wajen kai hari a kan wurare na farar hula, da makarantu da asibitoci da sauran cibiyoyi na jama’a.

A nasa bangaren, Fadi Alameh, Daraktan Asibitin Al-Sahel, ya yi Allah wadai da ikirarin Isra’ila, yana mai kiransu da bayanaai na karya da Isra’ila ta saba yi domin keta dokokin kasa da kasa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments