Turkiyye, Saudiyya, Pakistan, Iran, Zasu Ci Gaba Da Tattaunawa Kan Tsaro

Bangarorin sun bayyana hakan ne bayan taron da suka gudanar a Tehran kan sha'anin tsaro a yankin.

KasashenIran, Pakistan, Turkiyye da kuma Saudiyyasun cimma matsaya ta ci gaba da tattaunawa akan tsaron yankin.

Bangarorin sun bayyana hakan ne bayan taron da suka gudanar a Tehran ranar Litinin kan sha’anin tsaro a yankin.

Taron na Tehran ya mayar da hankali kan hadin gwiwa, ayyukan Isra’ila, da kuma abubuwan da ke faruwa a Falasdinu da Lebanon, yayin da Iran ta nuna shirye-shiryenta na warware duk wani sabani da kasashen Musulmi.

Batutuwan da suka shafi tsaron yankin, sakamakon hare-haren soji na Amurka da Isra’ila kan Iran, da kuma goyon bayan al’ummar Falasdinu da Lebanon sun kasance muhimman abubuwan da aka tattaunawa.

Kasar Pakistan ce ta ba da shawarar gudanar da taron, kuma an yi shi ne tare da goyon baya da hadin gwiwar kasar Iran.

Sakataren Majalisar Koli ta Tsaron Kasa ta Iran, Manjo Janar Mohsen Rezaei, shi ne ya karbi bakuncin taron.

Babban hafsan sojin kasa na Pakistan, Field Marshal Asim Munir, da Ministan Tsaron Saudiyya, Yarima Khalid bin Salman, da kuma Daraktan Hukumar Leken Asiri ta Turkiyya, Ibrahim Kalin, suka wakilci kasashensu a taron.

A cewar wata sanarwa ta hadin gwiwa da aka fitar bayan taron kasashen hudu a Tehran, Turkiyya, Saudiyya, Pakistan da Iran sun amince su ci gaba da tattaunawa da nufin karfafa hadin gwiwa kan batutuwan da suka shafi yankin, ciki har da batun zaman lafiya da tsaro.

A yayin taron, shugaban kasar Iran Massoud Pezeshkian ya bayyana cewa Iran a shirye take ta dauki matakai na zahiri don zurfafa hadin gwiwar yankin, warware sabani, da kuma karfafa alaka tsakanin kasashen da Musulmi suka fi yawa.

Ya kara da cewa Tehran tana goyon bayan duk wata fahimta da zata habaka hadin kan yankin, tsaro da ci gaba.

Pezeshkian ya ce kasashen Musulmi za su iya amfani da karfin haÉ—in gwiwarsu don gabatar wa duniya da wani tsari bisa adalci da ci gaba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted