Kotun manyan laifuka a kasar Tunisiya ta daure Shugaban kungiyar al-Nahdha ta masu kishin musulunci Rashid al-Ganushi, zaman kurkuku na tsawon shekaru 20.
Haka nan kuma an daure wata ‘yar Jarida Shahrizad Ukkasha wacce take wajen kasar, zaman kurkuku na tsawon shekaru 22.
Wata ‘yar jaridar da ita ma ta sami hukuncin dauri, ita ce Shuza Bilhaj, wacce za ta yi zaman kurkuku na tsawon shekaru5.
Shi kuwa tsohon minista Lutfi Zaitun an yanke masa hukuncin zaman kurkuku na shekaru 35, sai kuwa mai magana da yawun ma’aikatar harkokin cikin gida Muhammad Ali al-Aruri, shekaru 13 a gidan kaso. Yayin da tsohon shugaban gwamnatin kasar Hisham al-Mashishi zai yi zaman shekaru 35 a gidan kurkuku.
Tun a watan Disamba na 2021 ne aka bude sharia akan wadannan ‘yan siyasar, wacce ake wa kallon cewa ba ta da wani tushe na doka da ya wuce yi wa ‘yan siyasa bita da kulli.