Tsohon Shugaban Kungiyar Leken Asirin HKI ta “Shabak” ya ce: Ya kadu Saboda Yadda Majalisa Ta Kasa Tafiyar Da Harkokin Yaki

Tsohon shugaban hukumar leken asidin cikin HKI, ( Shabak) ya yi suka kakkausa akan Malisar HKI wacce ya ce, ta kasa tafiyar da yaki,lamarin da

Tsohon shugaban hukumar leken asidin cikin HKI, ( Shabak) ya yi suka kakkausa akan Malisar HKI wacce ya ce, ta kasa tafiyar da yaki,lamarin da ya ce, ya girgiza shi matuka.

Bugu da kari, tsohon shugaban hukumar leken asirin ta cikin HKI ya ce; A tarinsu ba a taba yin  majalisar da ta ci kasa kamar ta Fira minister  Benjamine Netanyahu ba, da haka ne ya kai ga afkuwar 7 ga watan Oktoba a fadarsa.

Haka nan kuma ya ce a  Babu wani abinda Netanyahu yake yi idan ba haddasa sabani da rabuwar akwuna a tsakanin Isra’ilawa ba.

 Har ila yau, tsohon shugaban kungiyar ta “Shabak” ya ce a halin yanzu HKI tana fuskantar barazanar rushewa ce,don haka tana da bukatuwa da sabuwar hanyar daga ciki da akwai kiran zaben gaggawa.

Tun bayan da Netenyahu ya rushe majalisar yaki ne dai ake cigaba da samun sabani da rikici a tsakanin ‘yan siysa da jami’an tsaron kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments