Tsohon Shugaban Amurka Joe Biden Ya Caccaki Trump Kan Rusa Kundin Tsarin Mulkin Kasar

Tsohon shugaban Amurka Joe Biden ya yi dirar mikiya da ba a taba ganin irinsa ba kan gwamnatin Trump! Tsohon shugaban kasar Amurka Joe Biden

Tsohon shugaban Amurka Joe Biden ya yi dirar mikiya da ba a taba ganin irinsa ba kan gwamnatin Trump!

Tsohon shugaban kasar Amurka Joe Biden ya yi gargadin cewa: Amurka na fuskantar “kwanaki masu duhu” a karkashin gwamnatin shugaba Donald Trump, yana mai zargin bangaren zartarwa da “rusa kundin tsarin mulkin kasar,” tare da dorawa Majalisa da Kotun Koli wani bangare na alhakinsu.

Biden ya bayyana hakan ne a wani jawabi da ya gabatar a birnin Chicago a wajen taron shekara-shekara na kungiyar lauyoyi ta kasa, inda ya yi jawabi ga lauyoyi da alkalai na Amurka baki daya.

Biden ya jaddada cewa; Gwamnatin Trump tana yin hakan, sau da yawa tare da taimakon Majalisa da ke zaune a gefe, da kuma ba da ikon kotun koli a ƙasar. “Allah ne ya san irin hukunce-hukuncen da mahukuntan Amurka suke zartarwa bisa radin kansu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted