Kona mutanen da suka rasa matsugunansu a cikin tantunansu, a cikin dare mai wahala ga zirin Gaza
Da sanyin safiyar Lahadi 14 ga watan Satumban shekara ta 2025 jiragen yakin haramtacciyar kasar Isra’ila suka ci gaba da kai munanan hare-haren bama-bamai a zirin Gaza, musamman birnin Gaza, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane da jikkata da dama. Sun kuma tayar da bama-bamai tare da tarwatsa gidaje da hasumiyai da nufin tilasta wa mazauna wurin tserewa tare da raba mafi yawan adadinsu da muhallinsu domin gudu zuwa tsakiya Gaza da kuma kudancin gabar tekun.
Majiyoyin lafiya a asibitin Al-Shifa sun ba da rahoton mutuwar wani Bafalasdine tare da jikkatar wasu a wani harin da sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan wata mota kusa da asibitin yammacin birnin Gaza. An kuma kashe wasu Falasdinawa hudu tare da jikkata wasu a lokacin da jiragen saman yakin sojin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai hare-hare kan tantunan da ke dauke da ‘yan gudun hijira a yammacin birnin.
Majiyoyin kiwon lafiya sun ce hare-haren bama-baman sojojin mamayar Isra’ila sun kai kan tantuna da makarantar da ke dauke da mutanen da suka rasa matsugunansu, yawancinsu mata da yara ne, lamarin da ya yi sanadin mutuwar da dama daga cikinsu, wadanda suka kone kurmus a cikin tantunansu a wani mummunan yanayi.