Trump: Za a iya cimma yarjejeniya da Iran a wata mai zuwa

Shugaban Amurka Donald Trump ya fadi a wannan  Alhamis cewa dole ne Amurka ta cimma yarjejeniya da Iran, idan kuma ba haka ba a cewarsa

Shugaban Amurka Donald Trump ya fadi a wannan  Alhamis cewa dole ne Amurka ta cimma yarjejeniya da Iran, idan kuma ba haka ba a cewarsa lamurran ba zasu yi kyau ba.

Ya bayyana hakan ne bayan ganawarsa da Firayim Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu.

A nasa bangaren, Netanyahu ya ce a cikin wata sanarwa a wannan  Alhamis cewa yana fatan kokarin Trump zai taimaka wajen samar da yanayin cimma yarjejeniya da Iran.

Abin tuni dai shi ne cewa Iran da Amurka sun yi tattaunawa a makon da ya gabata a Oman, kuma Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araqchi ya bayyana zaman a matsayin “mai armashi.”

Wannann a zuwa ne a daidai lokacin da Amurka da Isra’ila suke barazanar kai wa Iran da sunan rusa shirinta na makamashin nukiliya, ya yin da Iran din a nata bangaren ta bayyana cewa a shirye domin tunkarar kowace irin barazana ko shsihigi a kan kasarta da al’ummarta.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted