Trump Ya Yi Wa  Falasdinawa Jordan Da Masar Barazana Akan Yankin Gaza

Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi barazanar cewa matukar Falasdinawa ba su saki fursunonin  Isra’ila ba daga nan zuwa Asabar, to za a kawo

Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi barazanar cewa matukar Falasdinawa ba su saki fursunonin  Isra’ila ba daga nan zuwa Asabar, to za a kawo karshen tsagaita wutar yakin da aka yi, da komawa yaki.

Shugaban kasar ta Amurka ya shata wa’adin 12: 00 Na ranar Asabar a matsayin lokacin karshe na mika fursunonin.

Shugaban kasar ta Amurka wanda yake Magana da ‘yan jarida a ofis dinsa dake fadar White House, ya sake jaddada tsohuwar barazanar da ya yi tun kafin a rantsar da shi, na ce wa zai bude kofofin jahannama idan ba a mayar da fursunonin ba daga Gaza.”

Donald Trump ya kara da cewa, ya yi Magana da Benjamin Netanyahu akan wa’adin na karshe a ranar Asabar mai zuwa.

Dangane da batun fitar da Falasdinawa daga Gaza kuwa, shugaban kasar ta Amurka ya ce, ya yi imani da cewa Jordan za ta karbi Falasdinawan, tare da barazanar dakatar da taimakon da Amurka take bai wa kasar idan ba ta yi hakan ba.

Ita ma Kasar Masar ta fuskanci barazanar Amurka idan ba ta karbi Falasdinawan da Trump yake tunanin korarsu daga Gaza ba.

Shugaban kasar ta Amurka ya bayyana cewa, zai sayi yankin Gaza domin yin gine-gine na kasuwanci a ciki, lamarin da ya jawo masa mayar da martani daga sassa daban-daban na duniya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments