Rahotanni daga kasar Syria na cewa wata tawagar Majalisar Dinkin Duniya ta shiga birnin Jableh da ke yankin Latakia na kasar Siriya a karon farko a daren jiya Lahadi, kamar yadda wata majiya ta kasar ta shaida wa Al Mayadeen.
Tawagar ta Majalisar Dinkin Duniya sun zagaya a unguwannin Jableh, inda suka duba shaguna da gidajen jama’a da aka wawushe da kuma wadanda aka kona.
Wannan dai na zuwa ne bayan wani tashin hankali da ya barke a yammacin kasar ta Syria, inda aka ga wasu dauke da makamai masu alaka da ma’aikatar tsaron sabuwar gwamnatin kasar ta Syria da kuma dakarun tsaron cikin gida a cikin faifan bidiyo suna aikata munanan laifukan yaki da suka hada da kisan fararen hula da rana tsaka.
Tun bayan da gamayyar kungiyoyi masu dauke da makamai karkashin inuwar kungiyar Tahrir Sham mai alaka da kungiyar alkaida suka hambarar da gwamnatin Bashar Assad, suka fara aiwatar da kisa a bainar jama’a a kan tsiraru, bisa zargin cewa suna dad a alaka da gwamnatin Assad, amma lamarin ya kara tsanata a cikin ‘yan kwanakin nan.
Sakamakon tashin hankalin, an kashe ‘yan kasar Syria sama da 1,018, wadanda akasarinsu fararen hula ne, da suka hada da mata da kananan yara, a cewar wani rahoto da kungiyar kare hakkin bil’adama ta Syrian Observatory for Human Rights (SOHR) ta fitar, amma wasu bayanai daga bakunan mazauna yankunan da abin ya faru na nuni da cewa adadin ya zarta haka.