Tawagar fursinonin yaki na kasar Rasha daga kasar Ukrain sun koma gida, saboda yarjeniyar da kasashen biyu suka cimma a birnin Istambul na kasar Turkiyya.
Kamfanin dillancin labaran Spunik na kasar Rasha ya bayyana cewa a taro na biyu tsakanin jami’an gwamnatocin kasashen biyu a birnin Istambul na kasar Turkiya wato ranar 2 ga watan yunin da muke ciki ce suka cimma yarjeniyar musayar fursinonin a karo na biyu.
Labarin ya nakalto ministan tsaron kasar Rasha yana cewa fursinonin Rasha da suke hannun Ukraine sun isa kasar Rasha a jiya talata. Haka ma bangaren Rasha ta mikawa gwamnatin Ukraine wasu daga cikin fursinonin da suke hannunta.
Ministan ya kara da cewa a halin yanzu firsinonin suna kasar Belerus inda aka mikasu ga gwamnatin Belerus kuma suna ayyukan gwaji-gwaje likita don sanin lafiyansu.