Jaridar Politico wacce ake bugawa a Amurka ta nakalto wani jami’in diplomasiyyar turai wanda ya bukaci a sakaya sunansa yana cewa; Tarayyar turai din tana cikin Shirin kalubalantar shugaban Amurka Donald Trump matukar ya kwace iko da yankin Greenland na kasar Denmark.
Jami’in diplomasiyyar na turai ya kuma ta fara tattauna fito da tsarin da za ta yi aiki da shi idan har Trump din ya yi tunanin kai wa yankin na Greenland hari domin kwace shi, da zai hada da kai rundunar Nato a kusa da tsibirin.
Jami’in diplomasiyyar ya kara da cewa; Dole ne mu zama cikin Shirin yin fito na fito kai tsaye da Trump. Shi mutum ne mai halin fada da tsokana, don haka dole ne mu shirya.’
A ranar lahadin da ta gabata ne dai shugaban kasar ta Amurka Donald Trump ya fada wa jaridar “The Atlantic magazine” cewa; Amurka tana da bukatar tsibirin na Greenland.
Fira ministan kasar Denmark Mette Frederriksen ya yi kira ga Donald Trump da ya daina yin Magana akan yankin na Greenland haka.”
Shi ma tsohon fira ministan yankin na Greenland ya ce, yankin ba na sayarwa ba ne.
Har zuwa 1953, yankin na Greenland ya kasance a karkashin mulkin mallakar Denmark, said ai a 2009 yankin ya sami cin gashin kai,amma ya ci gaba da zama a karkashin masarautar Denmark, duk da cewa mazauna yankin ne ke tafiyar da harkokinsu na yau da kullum.